Zanga-Zanga Ta Jawo Ɗaukar Matakin Gwajin Shan Miyagun Ƙwayoyi, Akan Ɗaliban ATBU
Ɗalibai da Iyaye, na cigaba da bayyana rashin jindaɗinsu kan matakin da Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, da ke jihar Bauchi ta ɗauka, na tilasta yin gwajin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ga dukkannin Ɗaliban Jami’ar, da ke karatun Digirin farko.
Jami’ar dai, ta ɓullo da tsarin yin gwajin shaye-shayen ne, da nufin tantance haƙiƙanin ɗaliban da ke ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, duba da yadda ta ce ɗaliban sun gaza sarrafuwa ko bin umarni, a lokacin da su ka ƙudiri aniyar gudanar da zanga-zanga.
Sai dai, Ɗalibai da Iyaye da dama, su na cigaba da kokawa kan matakin, musamman ma duba da yawan kuɗaɗen da gwajin zai laƙume.
Jami’ar ta ATBU ta ɗauki wannan mataki ne kwanaki kaɗan bayan dawowa daga hutun makonni biyar da ta shiga, biyo bayan zanga-zangar da ɗaliban Jami’ar su ka gudanar, kan kisan wani ɗalibin aji biyar, da aka daɓawa wuƙa, ya yin da ya ke yunƙurin karɓo jakar budurwarsa da wasu ƴan daba su ka ƙwata.
Gwajin shan miyagun ƙwayoyin da hukumar makarantar marabci ɗalibai da shi, bayan komawa a ranar Lahadi dai, zai laƙumewa kowanne ɗalibi sama da Naira 10,000.
Ɗalibai da dama dai, sun ce ba su da halin biyan kuɗin gwajin, sakamakon rashin sanin matakin, har sai da su ka dawo makaranta.