Kotu

Zauren Dattijan Arewa Ya Bayyana Damuwa Kan Yunƙurin Sauya Akalar Fannin Shari’a

Zauren Dattijan Arewa (NEF), ya bayyana damuwa kan halin da al’amuran Shari’a su ka tsinci kansu, a halin yanzu.

Ta cikin wani jawabi da zauren ƙarƙashin Jagorancin, Farfesa Ango Abdullahi, ya fitar, da yammacin jiya, ya bayyana buƙatar ɓangaren shari’a da ya gujewa ƙauracewar sahihancinsa da al’umma su ka yi, yarda da shi, da ma ƙwarin gwuiwar da su ke da shi ga fannin.

Zauren ya ce, fannin shari’a na da gagarumar rawar takawa wajen tabbatar da samun adalci, kare haƙƙoƙin ƴan ƙasa, da ma tabbatar da ingancin sahihan zaɓukan da aka gudanar.

Ya na mai cewar, dukkannin wasu ayyuka da su ka fita daga cikin jerin waɗannan, to tabbas yunƙurin ciyar da Demokraɗiyya baya ne.

Zauren ya yi kira ga ɗaukacin Alƙalai da su kasance masu kwatanta gaskiya, a cikin ayyukansu, ta hanyar yin biyayya ga kundin dokokin ƙasa sau da ƙafa, ya na mai buga misali da tsohon Alƙalin Kotun Ƙoli, Mai Shari’a Dattijo Mohammed, ta hanyar bayyana irin gwagwarmayar da ya yi wajen fatattakar rashawa, a fannin shari’a.

Ka zalika ya ce, halin da ake ciki a yanzu abu ne da zai iya sanya al’umma komawa irin salon siyasar ko a mutu ko a yi rai.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button