Kasuwanci

Zawarawa Sama Da 500, Sun Amfana Da Tallafin Sana’a A Jihar Kaduna

Sama da Zawarawa 500 ne su ka rabauta da tallafin bunkasa sanaóí na Naira miliyan 37, domin kula da kansu, tare da Iyalansu, a jihar Kaduna.

An zabo zawarawan da su ka rabauta da tallafin ne daga mazabu 22 da ke gundumar tarayya ta kananan hukumomin Kachia da Kagarko, inda kowaccensu ta rabauta da Naira 30,000, ya yin da wadanda su ka gabatar da daftarin tsarin kasuwanci wato ‘Business Proposals’daga cikinsu su ka ci gajiyar Naira Dubu 300 zuwa Dubu 500.

Da ya ke jawabi, a ya yin rabon tallafin, Dan Majalissar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kachia da Kagarko, Gabriel Saleh Zock, ya bayyana rabon tallafin a matsayin guda daga cikin matakan da ya ke dauka, na saukakawa alúmma halin matsin tattalin arzikin da kasar nan ta tsinci kanta.

Zock din, ya kuma ce dukkannin wadanda su ka cimma nasara a kasuwancin nasu, za su rabauta da tallafin miliyan guda, bayan shekara daya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button