Zimbabwe Ta Ƙaddamar Da Gangamin Yaƙi Da Cholera
Kasar Zimbabwe ta kaddamar da gangamin allurar rigakafin cutar Cholera, inda ta ke fatan ba wa sama da yan kasar miliyan biyu rigakafin cutar, wacce ke yaduwa ta hanyar amfani da gurbataccen ruwan sha.
Allurar kuma, na bada kariyar tsawon watanni shida ne, ga dukkannin al’ummar da su ka rabauta da ita.
Tuni kuma aka fara ba da rigakafin daga yankin Kuwadzana da ke kusa da birnin Harare, ya yin da ma’aikatan lafiyar ke mayar da hankali kan kananan yara.
An samu barkewar wannan annoba a kasar ne dai, tun a watan Fabrairun 2023, inda ta yi sanadiyyar rasa rayukan sama da mutane 400, ya yin da dubu 20, su ka kamu da ita.
Zimbabwe za ta karbi, kimanin miliyan 2.3 na rigakafin daga cibiyar kula da kananan yara ta UNICEF, da hukumar lafiya ta duniya WHO, za kuma a jibge alluran rigakafin ne, a manyan biranen kasar 29.
Zuwa yanzu kuma, tuni aka rabar da sama da dubu 892 na rigakafin, kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar, ta bayyana.
Cholera dai, na yaduwa ne, sanadiyyar amfani da gurbataccen abinci ko ruwan sha, ta kuma fi hayayyafa a yankunan da ke da yawan jama’a, kamar birane, da wuraren da ke da karancin tsafta.